16. To, a ce ban nauyaya muku ba ɗin, ashe, sai ku ce dabara na yi muku, na shawo kanku ta hanyar yaudara!
17. Na cuce ku ne ta wurin wani daga cikin waɗanda na aiko a gare ku?
18. Na roƙi Titus ya je, na kuma aiko ɗan'uwan nan tare da shi. To, Titus ya cuce ku ne? Ashe, ba Ruhu ɗaya yake bi da mu ba, ni da shi? Ba kuma hanya ɗaya muke bi ba?
19. Ashe, tun dā tsammani kuke yi muna kawo hanzarinmu a gare ku ne? A'a, a gaban Allah muke magana, muna na Almasihu, wannan kuwa duk domin inganta ku ne, ya ku ƙaunatattu.
20. Ina tsoro kada watakila in na zo in same ku ba a yadda nake so ba, ku kuma ku gan ni ba a yadda kuke so ba, ko ma a tarar da jayayya, da kishi, da fushi, da sonkai, da yanke, da tsegunguma, da girmankai, da tashin hankali.