2 Kor 11:30-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30. In ma lalle ne in yi gadara, to, sai in yi taƙama da abubuwan da suke nuna raunanata.

31. Allahn Ubangiji Yesu, wato Ubansa, wanda ya yabo ya tabbata a gare shi har abada, ya sani ba ƙarya nake yi ba.

32. A Dimashƙu gwamnan da yake ƙarƙashin sarki Aretis ya tsare ƙofofin birnin Dimashƙu don ya kama ni,

33. amma sai aka zura ni a cikin babban kwando ta tagar garu, na kuɓuce masa.

2 Kor 11