3. Da farko dai lalle ne ku fahimci wannan, cewa a can zamanin ƙarshe masu ba'a za su zo suna ba'a, suna biye wa muguwar sha'awarsu,
4. suna cewa, “To, ina alkawarin dawowarsa? Ai, tun a lokacin da kakannin kakanninmu suka ƙaura, dukan abubuwa suna tafe ne kamar dā, tun farkon halitta.”
5. Da gangan suke goce wa maganar nan, cewa tun dā dā ta wurin maganar Allah sammai suka kasance, aka kuma siffata ƙasa daga ruwa, tana kuma a tsakiyar ruwa.
6. Ta haka ne kuma, duniyar wancan zamani, ruwa ya sha kanta, ta hallaka.