8. Domin daga gare ku ne aka baza Maganar Ubangiji, ba ma a ƙasar Makidoniya da ta Akaya kaɗai ba, har ma a ko'ina bangaskiyarku ga Allah ta shahara, har ma ya zamana, ba sai lalle mun faɗa ba.
9. Domin su da kansu suke ba da labarin irin ziyartarku da muka yi, da kuma yadda kuka rabu da gumaka, kuka juyo ga Allah, domin ku bauta wa Allah Rayayye na gaskiya,
10. ku kuma saurari komowar Ɗansa daga Sama, wanda ya tasa daga matattu, wato Yesu, mai kuɓutar da mu daga fushin nan mai zuwa.