1 Tar 9:2-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Waɗanda suka fara zama a biranen mallakarsu, su ne Isra'ilawa da firistoci, da Lawiyawa, da kuma ma'aikatan Haikali.

3. Waɗansu mutanen Yahuza, da na Biliyaminu, da na Ifraimu, da na Manassa suka zauna a Urushalima.

7. Ga zuriyar Biliyaminu a Urushalima bi da bi, da Sallai ɗan Meshullam, da Hodawiya, da Hassenuwa,

8. da kuma Ibneya ɗan Yeroham, da Ila ɗan Uzzi, wato jīkan Mikri, da Meshullam ɗan Shefatiya, da Reyuwel, da Ibnija.

9. Tare da danginsu a zamaninsu, sun kai ɗari tara da hamsin da shida ne. Duk waɗannan shugabannin gidajen kakanninsu ne.

10. Daga cikin firistoci masu zama a Urushalima su ne Yedaiya, da Yehoyarib, da Yakin,

1 Tar 9