74. Daga cikin kabilar Ashiru kuma an ba da Mishal duk da makiyayarta, da Abdon duk da makiyayarta,
75. da Helkat duk da makiyayarta, da Rehob duk da makiyayarta.
76. Daga na kabilar Naftali kuma an ba da Kedesh ta Galili duk da makiyayarta, da Hammon duk da makiyayarta, da Kartan duk da makiyayarta.
77. Daga na kabilar Zabaluna, an ba sauran Lawiyawa, wato 'ya'yan Merari, maza, Rimmon duk da makiyayarta, da Tabor duk da makiyayarta.