16. 'Ya'yan Lawi, maza, su ne Gershon, da Kohat, da Merari.
17. Waɗannan su ne sunayen 'ya'yan Gershon, maza, Libni da Shimai.
18. 'Ya'yan Kohat, maza, su ne Amram, da Izhara, da Hebron, da Uzziyel.
19. 'Ya'yan Merari, maza kuwa, su ne Mali da Mushi. Waɗannan su ne iyalan Lawiyawa bisa ga gidajen kakanninsu.
20. Zuriyar Gershon bi da bi, su ne Libni, da Yahat, da Zimma,