1 Tar 4:32-33-42 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Feniyel shi ne mahaifin Gedor, Ezer kuwa shi ne mahaifin Husha. Waɗannan su ne 'ya'yan Hur, maza, wato ɗan farin Efrata, zuriyarsa ne suka kafa Baitalami.

5. Ashur, wanda ya kafa Tekowa, yana da mata biyu, su ne Hela, da Nayara.

6. Nayara ta haifa masa Ahuzzam, da Hefer, da Temeni, da Hayahashtari. Waɗannan su ne 'ya'yan Nayara, maza.

7. 'Ya'yan Hela, maza, su ne Zeret, da Izhara, da Etnan.

8. Hakkoz shi ne mahaifin Anub, da Zobeba, shi ne kuma kakan iyalin da suka fito daga zuriyar Aharhel ɗan Harum.

9. Yabez ya fi sauran 'yan'uwansa kwarjini saboda haka mahaifiyarsa ta sa masa suna Yabez, wato da wahala ta haife shi.

32-33. Sun kuwa zauna a waɗansu wurare guda biyar, wato Itam, da Ayin, da Rimmon, da Token, da Ashan, da ƙauyukan da suke kewaye, har zuwa kudu maso gabas da garin Ba'al: Ga lissafin iyalansu da wuraren da suka zauna.

34-37. Meshobab, da Yamlek, da Yosha ɗan Amaziya,Yowel, da Yehu ɗan Yoshibiya, wato jīkan Seraiya, ɗan Asiyel,Eliyehoyenai, da Ya'akoba, da Yeshohaya, da Asaya, da Adiyel, da Yesimiyel, da Benaiya,Ziza ɗan Shifi, wato jīkan Allon, zuriyar Yedaiya, da Shimri ɗan Shemaiya.

38. Waɗannan da aka jera sunayensu, su ne shugabannin iyalansu da gidajen kakanninsu.Sun ƙaru ƙwarai.

39. Suka yi tafiya har zuwa mashigin Gedor, zuwa gabashin kwarin don nemar wa garkunansu makiyaya.

40. A can suka sami makiyaya mai kyau mai dausayi. Ƙasar kuwa tana da faɗi, babu fitina, sai salama, gama mazaunan wurin a dā Hamawa ne.

41. Waɗannan da aka lasafta sunayensu, su ne suka zo a kwanakin Hezekiya Sarkin Yahuza, suka fāɗa wa alfarwai da bukkoki waɗanda suka tarar a can, suka hallaka su sarai, sa'an nan suka maye wurinsu saboda akwai makiyaya domin garkunansu a wurin.

42. Waɗansu daga cikinsu, mutum ɗari biyar daga zuriyar Saminu, suka tafi wajen gabashin Edom. Waɗanda suka shugabance su kuwa, su ne 'ya'yan Ishi, wato Felatiya, da Neyariya, da Refaya, da Uzziyel.

1 Tar 4