1. 'Ya'yan Yahuza, maza, su ne Feresa, da Hesruna, da Karmi, da Hur, da Shobal.
2. Rewaiya ɗan Shobal, shi ne mahaifin Yahat. Yahat shi ya haifi Ahumai, da Lahad. Waɗannan su ne iyalin Zoratiyawa.
3. Waɗannan kuma su ne 'ya'yan Itam, Yezreyel, da Ishma, da Idbasha, da 'ya ɗaya, ita ce Hazzelelfoni.
4. Feniyel shi ne mahaifin Gedor, Ezer kuwa shi ne mahaifin Husha. Waɗannan su ne 'ya'yan Hur, maza, wato ɗan farin Efrata, zuriyarsa ne suka kafa Baitalami.
5. Ashur, wanda ya kafa Tekowa, yana da mata biyu, su ne Hela, da Nayara.
6. Nayara ta haifa masa Ahuzzam, da Hefer, da Temeni, da Hayahashtari. Waɗannan su ne 'ya'yan Nayara, maza.
7. 'Ya'yan Hela, maza, su ne Zeret, da Izhara, da Etnan.
8. Hakkoz shi ne mahaifin Anub, da Zobeba, shi ne kuma kakan iyalin da suka fito daga zuriyar Aharhel ɗan Harum.
9. Yabez ya fi sauran 'yan'uwansa kwarjini saboda haka mahaifiyarsa ta sa masa suna Yabez, wato da wahala ta haife shi.
10. Yabez ya roƙi Allah na Isra'ila, ya ce, “Ka sa mini albarka, ka faɗaɗa kan iyakata, hannunka kuma ya kasance tare da ni, ka kuma kiyaye ni daga abin da zai cuce ni.” Allah kuwa ya biya masa bukatarsa.