16. Eliyakim yana da 'ya'ya biyu maza, su ne Yekoniya, da Zadakiya.
17. 'Ya'yan Yekoniya wanda aka kama, su ne Sheyaltiyel,
18. da Malkiram, da Fedaiya, da Shenazzar, da Yekamiya, da Hoshama, da Nedabiya.
19. Fedaiya yana da 'ya'ya biyu maza, su ne Zarubabel da Shimai. 'Ya'yan Zarubabel, maza, su ne Meshullam, da Hananiya, da Shelomit 'yar'uwarsu,
20. da Hashuba, da Ohel, da Berikiya, da Hasadiya, da Yushab-hesed, su biyar ke nan.