31. Dukan waɗannan su ne masu lura da dukiyar sarki Dawuda.
32. Jonatan, kawun Dawuda, shi ne mai ba da shawara, yana da ganewa, shi kuma magatakarda ne. Shi da Yehiyel ɗan Hakmoni su ne masu koya wa 'ya'yan sarki, maza.
33. Ahitofel shi abokin shawarar sarki ne. Hushai Ba'arkite kuwa shi ne abokin sarki.
34. Sai Yehoyada ɗan Benaiya, da Abiyata suka gāji matsayin Ahitofel. Yowab shi ne babban shugaban sojojin sarki.