1. Ƙungiyoyin masu tsaron ƙofofi ke nan. Na wajen Kora shi ne Shallum ɗan Kore, daga cikin iyalin Ebiyasaf.
2. Shallum kuwa yana da 'ya'ya maza, su ne Zakariya, da Yediyayel, da Zabadiya, da Yatniyel,
3. da Elam, da Yehohanan, da Eliyehoyenai, su bakwai ke nan.
4. Obed-edom kuma Allah ya ba shi 'ya'ya maza, su ne Shemaiya, da Yehozabad, da Yowa, da Sakar, da Netanel,
5. da Ammiyel, da Issaka, da Fauletai, da su Allah ya sa masa albarka.
6. Ɗan farin Obed-edom, wato Shemaiya ya haifi 'ya'ya maza waɗanda suka yi shugabanci a gidan kakansu, gama su jarumawa ne.
7. 'Ya'yan Shemaiya, su ne Otni, da Refayel, da Obida, da Elzabad, waɗanda 'yan'uwansu, Elihu, da Semakiya jarumawa ne.