1 Tar 23:16-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Ɗan Gershom babba shi ne Shebuwel.

17. Ɗan Eliyezer shi ne Rehabiya, shugaba, shi Eliyezer ba shi da waɗansu 'ya'ya, amma Rehabiya yana da 'ya'ya da yawa.

18. Ɗan Izhara shi ne Shelomit, shugaba.

19. 'Ya'yan Hebron, maza, su ne Yeriya, shi ne babba, da Amariya na biyu, da Yahaziyel na uku, da kuma Yekameyam na huɗu.

20. 'Ya'yan Uzziyel, maza, su ne Mika, da Isshiya.

21. 'Ya'yan Merari, su ne Mali da Mushi. 'Ya'yan Mali su ne Ele'azara da Kish.

1 Tar 23