1. Bayan haka kuma Nahash Sarkin Ammonawa ya rasu, ɗansa kuma ya gāji sarautarsa.
2. Sa'an nan Dawuda ya ce, “Zan nuna alheri ga Hanun ɗan Nahash, gama tsohonsa ya nuna mini alheri.” Don haka Dawuda ya aiki manzanni su yi wa Hanun ta'aziyyar rasuwar tsohonsa.Fādawan Dawuda suka zo ƙasar Ammon wurin Hanun, domin su yi masa ta'aziyya.
3. Amma hakiman Ammonawa suka ce wa Hanun, “Kana tsammani Dawuda yana girmama tsohonka ne da ya aiko manzanni su yi maka ta'aziyya? Fādawansa sun zo wurinka ne don su leƙi asirin ƙasar, su bincike ta, su ci ta da yaƙi.”
4. Hanun kuwa ya kama fādawan Dawuda, ya aske gyammansu, ya yanyanke rigunansu a tsaka daga wajen kwankwaso, sa'an nan ya sallame su.
5. Waɗansu mutane kuwa suka je suka faɗa wa Dawuda abin da ya sami mutanen. Sai ya aiko a tarye su, gama an ƙasƙanta mutanen nan da gaske. Sai sarki ya ce, “Ku zauna a Yariko, har lokacin da gyammanku suka tohu sa'an nan ku iso.”