20. Abishai ɗan'uwan Yowab kuwa shi ne shugaban jarumawa talatin ɗin. Ya girgiza mashinsa, ya kashe mutum ɗari uku. Ya yi suna a cikin jarumawan nan talatin.
21. Cikin jarumawa talatin ɗin, shi ya shahara har ya zama shugabansu. Amma duk da haka bai kai ga jarumawan nan uku ba.
22. Benaiya ɗan Yehoyada, ɗan wani jarumi ne daga Kabzeyel, ya yi manyan ayyuka, ya kashe jarumawa biyu na Mowabawa. Sai ya gangara ya kashe zaki a cikin rami a ranar da ake yin dusar ƙanƙara.
23. Sai kuma ya kashe wani dogon Bamasare mai tsayi kamu biyar. Bamasaren yana da māshi mai kama da dirkar masaƙa a hannunsa, amma sai ya gangaro wurinsa da kulki a hannu, ya ƙwace māshin daga hannun Bamasaren, ya kashe shi da shi.
24. Waɗannan abubuwa Benaiya ɗan Yehoyada ya yi su, ya kuwa yi suna kamar manyan jarumawan nan uku.