1 Tar 1:8-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. 'Ya'yan Ham, maza, su ne Kush, da Mizrayim, da Fut, da Kan'ana.

9. 'Ya'yan Kush, maza, su ne Seba, da Hawila, da Sabta, da Ra'ama, da Sabteka. 'Ya'yan Ra'ama, maza, su ne Sheba da Dedan.

10. Kush shi ne mahaifin Lamirudu wanda shi ne ya fara ƙasaita a duniya.

11. Mizrayim shi ne mahaifin jama'ar Ludawa, da Anamawa, da Lehabawa, da Naftuhawa,

12. da Fatrusawa, da Kasluhawa tushen Filistiyawa ke nan, da Kaftorawa.

13. Kan'ana shi ne mahaifin Sidon ɗan farinsa, da Het,

14. da Yebusiyawa, da Amoriyawa, da Girgashiyawa,

15. da Hiwiyawa, da Arkiyawa, da Siniyawa,

16. da Arwadiyawa, da Zemariyawa, da Hamatiyawa.

17. 'Ya'yan Shem, maza, su ne Elam, da Asshur, da Arfakshad, da Lud, da Aram, da Uz, da Hul, da Geter, da Meshek.

1 Tar 1