1 Sar 8:54-63 Littafi Mai Tsarki (HAU)

54. Da Sulemanu ya gama wannan addu'a da roƙo ga Ubangiji, sai ya tashi daga gaban bagaden Ubangiji, inda yake a durƙushe da hannuwansa a miƙe zuwa sama.

55. Ya tsaya, ya sa wa taron jama'ar Isra'ila albarka da babbar murya, ya ce,

56. “Yabo ya tabbata ga Ubangiji wanda ya hutar da jama'arsa, Isra'ilawa, bisa ga yadda ya alkawarta. Daga cikin abin da ya alkawarta duka na alheri ba ko ɗaya da bai cika ba, kamar yadda ya alkawarta wa bawansa, Musa.

57. Ya Ubangiji Allah, sai ka kasance tare da mu kamar yadda ka kasance tare da kakanninmu, kada ka rabu da mu, ko ka yashe mu.

58. Ka sa zukatanmu su juyo gare ka, mu yi tafiya cikin tafarkunka, mu kiyaye umarnanka, da ka'idodinka da dokokinka, waɗanda ka umarci kakanninmu.

59. Ya Ubangiji Allahnmu, ka sa wannan roƙo da na yi ya kasance a gabanka, dare da rana. Ka biya bukatar bawanka, da bukatar jama'arka, Isra'ila, ta kowace rana,

60. domin dukan al'umman duniya su sani Ubangiji shi kaɗai ne Allah, banda shi, ba wani.

61. Ku kuma jama'arsa, sai ku amince da Ubangiji Allahnmu da zuciya ɗaya, ku kiyaye dokokinsa da umarnansa, kamar yadda kuke yi a yau.”

62. Sa'an nan sarki Sulemanu, tare da Isra'ilawa duka, suka miƙa sadaka ga Ubangiji.

63. Sulemanu kuwa ya miƙa wa Ubangiji hadaya ta salama da bijimai dubu ashirin da dubu biyu (22,000) da tumaki dubu ɗari da dubu ashirin (120,000). Ta haka sarki da dukan mutanen Isra'ila suka keɓe Haikalin Ubangiji.

1 Sar 8