1. Sai Sulemanu ya sa dattawan Isra'ila duka, da shugabannin kabilai, da shugabannin dangi dangi na Isra'ila, su hallara a gabansa a Urushalima, domin su kawo akwatin alkawari na Ubangiji daga Sihiyona, birnin Dawuda, zuwa Haikali.
2. Dukan jama'ar Isra'ila suka taru gaban sarki Sulemanu, wurin biki a watan Etanim, wato wata na bakwai.
3. Dukan dattawan Isra'ila suka zo, sai firistoci suka É—auki akwatin alkawarin,