Ya kafa ginshiƙan a shirayin Haikalin. Ya kafa ginshiƙi ɗaya a wajen dama, ya sa masa suna, Yakin, wato Allah ya kafa. Ya kafa ɗaya ginshiƙin a wajen hagu, ya sa masa suna Bo'aza, wato da ƙarfin Allah.