Sulemanu ya dalaye cikin Haikalin da zinariya tsantsa. Ya kuma gifta sarƙoƙin zinariya a gaban Wuri Mafi Tsarki na can ciki, sa'an nan ya dalaye su da zinariya.