7. Yanzu, ya Ubangiji Allahna, ka naɗa ni sarki, a matsayin Dawuda, tsohona, ko da yake ni yaro ne ƙarami, ban ƙware ba.
8. Ga ni kuwa a tsakiyar jama'arka wadda ka zaɓa, jama'a mai yawa wadda ba ta ƙidayuwa saboda yawansu.
9. Domin haka ka ba ni hikima ta yi wa jama'arka shari'a, domin in rarrabe tsakanin nagarta da mugunta, gama wane ni in iya mallakar jama'arka mai yawa haka?”