1. Aka yi shekara uku ba a yi yaƙi tsakanin Suriya da Isra'ila ba.
2. A shekara ta uku ɗin, sai Yehoshafat, Sarkin Yahuza, ya ziyarci Sarkin Isra'ila.
3. Sarkin Isra'ila kuwa ya ce wa fādawansa, “Ko kun sani Ramot-gileyad tamu ce, ga shi kuwa, mun yi shiru, ba mu ƙwace ta daga hannun Sarkin Suriya ba?”
4. Ya kuma ce wa Yehoshafat, “Za ka tafi tare da ni zuwa wurin yaƙi a Ramot-gileyad?”Yehoshafat ya amsa wa Sarkin Isra'ila, “Ni da kai ɗaya ne, mutanena kuma mutanenka ne, dawakaina kuma naka ne.”
5. Yehoshafat ya ce wa Sarkin Isra'ila, “Ka nemi faɗar Ubangiji tukuna.”
6. Sa'an nan Sarkin Isra'ila ya tara annabawa ɗari huɗu, ya tambaye su, ya ce, “In tafi in yi yaƙi da Ramot-gileyad, ko kuwa kada in tafi?”Su kuwa suka ce masa, “Ka haura, gama Ubangiji zai ba da ita a hannunka.”
7. Amma Yehoshafat ya ce, “Ba wani annabin da za mu tambaya kuma?”