41. Annabin ya yi saurim, ya kware ƙyallen a fuskarsa, sa'an nan sarki ya gane, ashe, ɗaya daga cikin annabawa ne.
42. Sa'an nan annabin ya ce wa sarki, “Ubangiji ya ce, ‘Da yake ka bar mutumin da na ƙaddara ga mutuwa ya kuɓuta daga hannunka, haka ranka zai zama a maimakon nasa, mutanenka kuwa a maimakon mutanensa.’ ”
43. Sarkin Isra'ila kuwa ya tafi gidansa a Samariya da baƙin ciki.