1 Sar 14:1-2 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A lokacin nan Abaija ɗan Yerobowam ya kwanta ciwo.

2. Yerobowam kuwa ya ce wa matarsa, “Ki tashi, ki ɓad da kama don kada a sani ke matata ce, sa'an nan ki tafi Shilo wurin Ahija, annabin nan wanda ya ce mini zan sarauci jama'an nan.

1 Sar 14