1 Sar 13:16-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Amma annabin ya ce, “Ba zan koma tare da kai ba, ba kuwa zan shiga gida ba, ko in ci abinci, ko in sha ruwa tare da kai a wannan wuri,

17. gama Ubangiji ya ce mini kada in ci abinci, ko in sha ruwa a can, ko in koma ta hanyar da na zo.”

18. Sa,an nan tsohon annabin ya ce masa, “Ai, ni ma annabi ne kamarka. Ubangiji ya yi mini magana ta bakin wani mala'ika, ya ce mini in komar da kai gidana don ka ci abinci, ka sha ruwa.” Amma ƙarya ce ya yi masa.

19. Saboda haka sai annabin ya koma tare da shi, ya ci abinci, ya sha ruwa a gidan tsohon annabin.

20. Sa'ad da suke zaune wurin ci, sai maganar Ubangiji ta zo ga tsohon annabin da ya komar da annabin Allah,

21. sai ya kira annabin Allah, wanda ya zo daga Yahuza, ya ce, “Ubangiji ya ce, ‘Da yake ba ka yi biyayya da maganar Ubangiji ba, ba ka kuma kiyaye umarnin da Ubangiji Allahnka ya umarce ka da shi ba,

22. amma ka komo, ka ci abinci, ka sha ruwa a wurin da ya ce maka, kada ka ci abinci, ko kuwa ka sha ruwa, saboda haka ba za a binne gawarka a kabarin kakanninka ba.’ ”

23. Bayan da ya ci abinci, ya sha sai tsohon annabin ya ɗaura wa jaki shimfiɗa don annabin da ya komo da shi.

24. Sa'ad da annabin Allah ya tafi, sai zaki ya gamu da shi a hanya, ya kashe shi, ya jefar da gawarsa a kan hanya. Sai jakin da zakin suka tsaya kusa da gawar.

25. Mutane suka wuce, suka ga gawar a kan hanya, da zaki a tsaye kusa da gawar. Suka tafi suka faɗa a birni, inda tsohon annabin nan yake.

26. Sa'ad da tsohon annabin nan ya ji, sai ya ce, “Wannan annabin Allah ne, wanda bai yi biyayya da maganar Ubangiji ba, saboda haka Ubangiji ya bashe shi ga zaki ya yayyage shi, ya kashe shi, kamar yadda Ubangiji ya faɗa masa.”

27. Sa'an nan ya ce wa 'ya'yansa maza, “Ku ɗaura mini shimfiɗa.” Su kuwa suka ɗaura,

28. ya hau ya tafi, ya iske gawar a hanya. Jakin da zakin suna tsaye kusa da gawar. Zakin bai ci gawar ba, bai kuma fāɗa wa jakin ba.

1 Sar 13