1 Sar 11:41-43 Littafi Mai Tsarki (HAU)

41. Sauran ayyukan Sulemanu, da dukan abin da ya yi, da hikimarsa an rubuta su a littafin tarihin Sulemanu.

42. Sulemanu ya yi shekara arba'in yana sarauta a Urushalima a kan Isra'ila duka.

43. Sulemanu ya rasu, aka binne shi a birnin Dawuda, wato Urushalima. ‘Dansa Rehobowam ya gaji sarautarsa.

1 Sar 11