5. Sama'ila kuma ya ce, “Ku tattara dukan Isra'ilawa a Mizfa, ni kuwa zan yi addu'a ga Ubangiji dominku.”
6. Isra'ilawa fa suka taru a Mizfa, suka kawo ruwa, suka zuba a gaban Ubangiji. Suka yi azumi a ranan nan, suka ce, “Mun yi wa Ubangiji zunubi.” Sama'ila kuwa ya zauna a Mizfa ya yi mulkin Isra'ilawa.
7. Da Filistiyawa suka ji Isra'ilawa sun taru a Mizfa, sai sarakunan Filistiyawa, su biyar, suka tafi, su yi yaƙi da Isra'ilawa. Sa'ad da Isra'ilawa suka ji labari, sai suka tsorata,
8. suka ce wa Sama'ila, “Ka yi ta roƙo ga Ubangiji Allahnmu don ya cece mu daga hannun Filistiyawa.”