1 Sam 30:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sa'ad da Dawuda da mutanensa suka koma Ziklag a rana ta uku, sai suka tarar Amalekawa sun riga sun kawo wa Negeb da Ziklag hari. Suka cinye Ziklag, suka ƙone ta.

2. Suka kwashe mata da dukan waɗanda suke ciki manya da ƙanana, suka tafi da su. Ba su kashe kowa ba, amma suka kwashe su, suka tafi.

3. Da Dawuda da mutanensa suka ga an ƙone garin, an kuma kwashe matansu, da 'ya'yansu mata da maza ganima,

4. sai suka yi ta kuka da ƙarfi, har ƙarfinsu ya ƙare.

1 Sam 30