10. Idan Akish ya tambayi Dawuda, “A ina ka kai hari yau?” Sai ya ce, “Na kai hari a Negeb ta Yahuza, ko Negeb ta Yerameyel, ko Negeb ta Ƙan'aniyawa.”
11. Dawuda bai bar mace ko namiji da rai ba, wato da zai kawo labari, a Gat, domin yana gudun kada su faɗi abin da yake yi, su ce, “Ga abin da Dawuda ya yi.” Abin da Dawuda ya yi ta yi ke nan a lokacin da yake zaune a ƙasar Filistiyawa.
12. Akish kuwa ya amince da Dawuda, yana cewa, “Ya mai da kansa abin ƙi ga mutanensa Isra'ilawa, zai zama barana muddin ransa.”