1 Sam 20:8-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. kai kuwa ka nuna mini alheri, gama ka yi mini alkawari mai ƙarfi. Amma idan ina da laifi, sai ka kashe ni da kanka. Don me za ka bar mahaifinka ya kashe ni?”

9. Jonatan ya masa ya ce, “Allah ya sawwaƙe! Da na sani babana yana da nufi ya yi maka mugunta, ai, da na faɗa maka.”

10. Sa'an nan Dawuda ya ce wa Jonatan, “Wane ne zai faɗa mini idan mahaifinka ya amsa maka da fushi?”

11. Jonatan kuwa ya ce masa, “Zo mu tafi saura.” Sai su biyu suka tafi saura.

12. Sa'an nan Jonatan ya ce wa Dawuda, “Ubangiji Allah na Isra'ila zai zama shaida. Gobe war haka, ko jibi zan tattauna maganar da mahaifina, idan da nufin alheri zuwa gare ka, zan aika, in faɗa maka.

13. Amma idan har mahaifina yana da niyyar yi maka mugunta, amma ban sanar da kai ba, to, bari Ubangiji ya hukunta ni. Ubangiji ya kasance tare da kai kamar yadda ya kasance da mahaifina.

14. Ba lokacin da nake da rai ne kaɗai za ka nuna mini alherin Ubangiji domin kada in mutu ba.

15. Ko bayan raina kada ka daina nuna wa gidana alheri har abada, lokacin da Ubangiji ya datse maƙiyanka daga fuskar duniya.”

16. Jonatan ya yi alkawari da gidan Dawuda. Ubangiji kuwa zai ɗauki fansa a kan maƙiyan Dawuda.

17. Sai Jonatan ya sa Dawuda ya yi masa alkawari zai ƙaunace shi, gama shi kansa yana ƙaunar Dawuda ƙwarai kamar yadda yake ƙaunar kansa.

18. Sa'an nan Jonatan ya ce wa Dawuda, “Gobe ce amaryar wata, ba kowa a wurin zamanka ke nan da yake ba za ka zo ba.

19. A rana ta uku za a gane ba ka nan sosai, to, sai ka tafi, ka ɓuya a wurin da ka ɓuya a waccan rana. Ka zauna kusa da tarin duwatsu.

20. Zan harba kibau guda uku kusa da tarin duwatsun, kamar ina harbin wani abu ne.

21. Zan aiki yaro ya tafi ya nemo kiban. Idan na ce masa, ‘Duba, ga kiban kusa da kai, ka kawo su,’ To, sai ka fito, ka zo, wato lalle kome lafiya ke nan, ba abin da zai cuce ka.

22. Amma idan na ce wa yaron, ‘Duba, kiban suna a gabanka,’ To, ka tafi, gama Ubangiji ya sallame ka, ka tafi.

23. A kan alkawarin da muka yi, ni da kai kuwa, Ubangiji shi ne shaida a tsakaninmu har abada.”

24. Dawuda ya ɓuya a saura. A ranar amaryar wata kuwa sarki ya zauna domin cin abinci.

25. Ya zauna inda ya saba zama kusa da bango. Jonatan ya zauna daura da shi, Abner kuwa ya zauna kusa da Saul, amma ba kowa a wurin zaman Dawuda.

1 Sam 20