1. Da Dawuda ya gama magana da Saul, sai zuciyar Jonatan ta saje da ran Dawuda. Jonatan kuwa ya ƙaunaci Dawuda kamar kansa.
2. Daga ran nan Saul ya riƙe Dawuda, bai bari Dawuda ya koma gidan mahaifinsa ba.
3. Jonatan kuma ya yi dawwamammen alkawari da Dawuda, domin shi, wato Jonatan, yana ƙaunar Dawuda kamar kansa.
26-27. Da fādawan suka faɗa wa Dawuda abin da Saul ya ce, sai Dawuda ya ji daɗi ƙwarai ya zama surukin sarki. Kafin lokacin da aka yanka masa ya yi, sai Dawuda ya tashi, ya tafi tare da mutanensa, suka kashe Filistiyawa ɗari biyu. Ya kawo loɓarsu duka, aka ba sarki, domin ya zama surukin sarki. Saul kuwa ya aurar da Mikal, 'yarsa, ga Dawuda.
28-29. Da Saul ya gane lalle Ubangiji yana tare da Dawuda, Mikal 'yarsa kuma tana ƙaunar Dawuda, sai ya ƙara jin tsoronsa, ya maishe shi maƙiyinsa na din din din.