6. Sa'an nan Ruhun Ubangiji zai sauko maka, za ka kuwa yi rawa da sowa tare da su, za ka zama wani mutum dabam.
7. Sa'ad da waɗannan alamu suka cika, sai ka yi abin da hali ya nuna maka, gama Ubangiji yana tare da kai.
8. Za ka riga ni zuwa Gilgal inda zan zo in miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama. Sai ka jira ni kwana bakwai, har in zo in sanar da kai abin da za ka yi.”
9. Da Saul ya juya zai tashi daga wurin Sama'ila, sai Ubangiji ya ba shi sabuwar zuciya. Alamun nan kuma suka cika a ranar.
10. Sa'ad da suka iso Gileyad, sai suka tarar da ƙungiyar annabawa. Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko a kansa da iko, sai ya shiga rawa da sowa tare da su.