8. Abinci ba zai ƙare mu a game da Allah ba. In mun ci, ba mu ƙaru ba, in kuma ba mu ci ba, ba mu ragu ba.
9. Sai dai ku lura, kada 'yancin nan naku ya zama abin sa tuntuɓe ga waɗanda ba su tsai da zuciyarsu ba.
10. Amma in wani mutum, wanda yake da rarraunan lamiri, ya gan ka, kai da kake da sani, kana ci a ɗakin gunki, ashe, wannan ba zai ƙarfafa lamirinsa har ya ci abincin da aka miƙa wa gunki ba?
11. Wato, ta sanin nan naka, sai a rushe rarraunan nan, ɗan'uwa ne kuwa wanda Almasihu ya mutu dominsa!
12. Ta haka ne kuke yi wa Almasihu laifi, wato ta wurin yi wa 'yan'uwanku laifi, kuna rushe rarraunan lamirinsu.
13. Saboda haka in dai cin nama ya sa ɗan'uwana tuntuɓe, har abada ba zan ƙara cin nama ba, don kada in sa ɗan'uwana tuntuɓe.