1 Kor 8:6-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. duk da haka dai, a gare mu kam, Allah ɗaya ne, wato Uba, wanda dukkan abubuwa suke daga gare shi, wanda mu kuma zamansa muke yi, Ubangiji kuma ɗaya ta gare shi muka kasance.

7. Amma dai ba kowa ne yake da wannan sani ba. Amma waɗansu ta wurin sabawarsu da al'amuran gunki har yanzu, sukan ci naman da suka ɗauka kamar an yanka wa gunki ne. Saboda haka lamirinsu, da yake rarrauna ne, ya ƙazantu.

8. Abinci ba zai ƙare mu a game da Allah ba. In mun ci, ba mu ƙaru ba, in kuma ba mu ci ba, ba mu ragu ba.

1 Kor 8