11. Wato, ta sanin nan naka, sai a rushe rarraunan nan, ɗan'uwa ne kuwa wanda Almasihu ya mutu dominsa!
12. Ta haka ne kuke yi wa Almasihu laifi, wato ta wurin yi wa 'yan'uwanku laifi, kuna rushe rarraunan lamirinsu.
13. Saboda haka in dai cin nama ya sa ɗan'uwana tuntuɓe, har abada ba zan ƙara cin nama ba, don kada in sa ɗan'uwana tuntuɓe.