1. To, yanzu a game da abubuwan da aka yanka wa gumaka, mun sani dukanmu muna da ilimi. Ilimi yakan kumbura mutum, ƙauna kuwa takan inganta shi.
2. Duk mai gani ya san wani abu, ai, har a yanzu, bai san yadda ya kamata ya sani ba.
3. In kuwa wani na ƙaunar Allah, to, Allah ya san shi.
4. A game da cin abin da aka yanka wa gumaka kuwa, mun sani, duk duniyar nan gunki yana a matsayin abin da babu ne, da kuma, babu wani Allah sai ɗaya.
5. Ko da yake, akwai waɗanda ake kira alloli a sama ko a ƙasa, don kuwa akwai “alloli” da “iyayengiji” da yawa,