20. Kowa yă zauna a maƙamin da Allah ya kiraye shi.
21. In ya kira ka kana bawa, kada ka damu. In kuwa kana iya samun 'yanci, ai, sai ka samu.
22. Wanda aka kiraye shi ga tafarkin Ubangiji yana bawa, ai, 'yantacce ne na Ubangiji. Kuma, wanda aka kira shi yana ɗa, bawa ne na Almasihu.
23. Da tamani aka saye ku. Kada fa ku zama bayin mutane.
24. To, 'yan'uwa, duk halin da aka kira mutum a ciki, sai yă zauna a kai, yana zama tare da Allah.
25. A game da matan da ba su yi aure ba kuwa, ba ni da wani umarnin Ubangiji, amma ina ba da ra'ayina ne a kan ni amintacce ne, bisa ga jinƙan Ubangiji.
26. Na dai ga ya yi kyau mutum yă zauna yadda yake, saboda ƙuncin nan da yake gabatowa.
27. In da igiyar aure a wuyanka, to, kada ka nemi tsinkewa. In kuwa ba igiyar aure a wuyanka, to, kada ka nemi aure.
28. Amma kuwa in ka yi aure, ba ka yi zunubi ba, ko budurwa ma ta yi aure, ba ta yi zunubi ba. Duk da haka dai, duk masu yin aure za su ji jiki, niyyata kuwa in sawwaƙe muku.