1 Kor 7:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. To, a yanzu, a game da abin da kuka rubuto, yana da kyau mutum ya zauna ba aure.

2. Amma don gudun fasikanci sai kowane mutum ya kasance da matarsa, kowace mace kuma da mijinta.

3. Miji yă ba matarsa hakkinta na aure, haka kuma matar ga mijinta.

1 Kor 7