20. Har wa yau, “Ubangiji ya san tunanin masu hikima banza ne.”
21. Saboda haka kada kowa yă yi fariya da 'yan adam. Don kuwa kome naku ne,
22. ko Bulus, ko Afolos, ko Kefas, ko duniya, ko rai, ko mutuwa, ko abubuwan yanzu, ko da na gaba, ai, duk naku ne.
23. Ku kuwa na Almasihu ne, Almasihu kuma na Allah ne.