7. Ba sona ne in gan ku a yanzu in wuce kawai ba, a'a, ina sa zuciya ma in yi kwanaki a wurinku, in Ubangiji ya yarda.
8. Amma zan dakata a Afisa har ranar Fentikos.
9. Don kuwa, an buɗe mini wata hanya mai fāɗi ta yin aiki mai amfani, akwai kuma magabta da yawa.
10. In Timoti ya zo, ku tabbata ya sami sakewa a cikinku, domin aikin Ubangiji yake yi kamar yadda nake yi.
11. Kada fa kowa yă raina shi. Ku raka shi lafiya, ya komo a gare ni, domin ina duban hanyarsa tare da 'yan'uwa.