1. To, a yanzu kuma ga zancen ba da gudunmawa ga tsarkaka, kamar yadda na umarci ikilisiyoyin Galatiya, haka ku ma za ku yi.
2. A kowace ranar farko ta mako, kowannenku ya riƙa tanada wani abu, yana ajiyewa gwargwadon samunsa, kada sai na zo tukuna, a tara gudunmawa.
3. Sa'ad da na iso, sai in aiki waɗanda kuka amince da su da wasiƙa, su kai taimakonku Urushalima.