1 Kor 15:45-47 Littafi Mai Tsarki (HAU)

45. Haka kuma yake a rubuce, “Mutumin farko, Adamu, ya zama rayayyen taliki,” Adamun ƙarshe kuwa Ruhu ne mai rayarwa.

46. Amma ba shi na Ruhun nan ne ya fara bayyana ba, na mutuntaka ne, daga baya kuma sai na Ruhu.

47. Mutumin farko daga ƙasa yake, na turɓaya ne. Na biyun kuwa daga Sama yake.

1 Kor 15