11. To, ko ni ne dai, ko kuma su ne, haka muke wa'azi, ta haka kuma kuka gaskata.
12. To, da yake ana wa'azin Almasihu a kan an tashe shi daga matattu, ƙaƙa waɗansunku suke cewa, babu tashin matattu?
13. In dai babu tashin matattu, ashe, ba a ta da Almasihu ba ke nan.
14. In kuwa ba a ta da Almasihu ba, to, ashe, wa'azinmu a banza ne, bangaskiyarku kuma banza ce.
15. Sai ma ya zamana mun yi wa Allah shaidar zur ke nan, domin mun shaida Allah, cewa ya ta da Almasihu, wanda kuwa bai tasar ba, in da gaskiya ne ba a ta da matattu.