1 Kor 14:38-40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

38. In kuwa wani ya ƙi kula da wannan, shi ma sai a ƙi kula da shi.

39. Saboda haka, 'yan'uwa, sai ku himmantu ga samun baiwar yin annabci, kada kuma ku hana yin magana da waɗansu harsuna.

40. Sai dai a yi kome ta hanyar da ta dace, a shirye kuma.

1 Kor 14